A rahoton wata wata na shirin yaki da yunwa wato Early Warning Systems ko kuma (FEWS Net) a takaice, rahoton ya ce faduwar damina a kurarren lokaci na daga cikin matsotsolin dake haifar da gibi inda hakan ke haddasa fari a kasahen na gabashin Afrika.
Matsalar farin da aka fuskanta a kasashen gabashin Afrika a shekarar 2016, ya haddasa matsalar karancin abinci a kasashen da dama dake yankin na Afrika.
Amma wannan rahoto ya bayyana cewa, karuwar ruwan sama da aka samu a yan kwanakin nan ya inganta makomar amfanin gonar a kasashen Kenya, Uganda, Rwanda, Burundi, Demokaradiyyar Congo, da arewacin Tanzania.
Sai dai kuma, a wasu yankuna na kudanci Somalia da wasu sassa gonaki na kudu maso gabashin Kenya, rashin samun yabanya ya ta'allaka ne da rashin faduwar damina a kan lokaci shi ya sa ake samun matsalar rashin ingatattun amfanin gona. (Ahmad)