in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta samar da ruwan sha ga mazauna Abidjan miliyan 2
2015-03-03 10:53:33 cri

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya kaddamar a ranar Litinin a Bonoua dake kudu maso gabashi, mai tazarar kilomita 35 daga birnin Abidjan da bude wani gidan ruwa domin samar da ruwan sha masu tsabta ga mazauna birnin Abidjan fiye da miliyan biyu.

Aikin da ya shafe Sefa biliyan 59, wanda a ciki biliyan 50 sun fito daga kasar Sin, na da manufar karfafa tsarin samar da ruwan sha ga birnin Abidjan da sauran birane da ke kewaye. Yankin da aka dauka shi ne kudancin Abidjan, musammun ma tsibirin Petit-Bassam, Koumassi, Marcory, Treichville, Port-Bouet mai yawan al'umma kusan miliyan 2, har ma gami da al'ummomin Grand-Bassam da Alepe.

Gidan ruwan na Bonoua dai zai rika samar da mita cuba 80000 a ko wace rana, shi ne na matakin farko na babban aikin da ya shafi Sefa biliyan 100 wanda zai taimaka a karshe wajen samar da mita cuba 740000 a ko wace rana a shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China