in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai matukar bukatar kara kaimi ga samar da tsaftacaccen ruwa da muhalli a Afirka
2015-01-30 10:36:58 cri

Shugaban majalissar ministocin kungiyar AU game da samar da ruwa ko AMCOW a takaice Mansour Faye, ya yi kira ga kasashen nahiyar Afirka da su kara yawan kudaden da suke samarwa, wajen aikin samar da tsaftacaccen ruwan sha da tsaftar muhalli.

Mr. Faye ya gabatar da wannan bukata ne yayin wani zaman tattaunawa game da kudurin Kigali, mai nasaba da bunkasa sha'anin samar da tsaftacaccen ruwan sha da tsaftar muhalli a Afirka, a ci gaba da gudanar babban taron AU na bana, wanda aka bude a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Faye ya kara da cewa, daukar matakan bunkasa wannan fanni, za su taimaka matuka, wajen magance barkewar cututtuka, da sauran manyan matsalolin dake addabar al'ummun Afirka.

Ya ce, kamata ya yi mahukuntan kasashen Afirka su fifita wannan fanni, ta yadda zai samu kulawa irin wadda ake baiwa fannin tsaro, da sauran muhimman fannonin ci gaba.

Kaza lika shugaban na AMCOW ya bayyana aniyar majalissar, ta gabatarwa shuwagabannin nahiyar Afirka wani daftari, mai kunshe da kudurorin kyautata tsaftar muhalli da samar da tsaftacaccen ruwan sha a daukacin nahiyar.

An dai kaddamar da kudurin Kigali ne a watan Yulin bara, da nufin farfado da manufar samar da kudaden inganta samar da ruwa da tsaftar muhalli.

Tuni kuma bankin raya Afirka ya alkawarta samar da zunzurutun kudi har dala miliyan 350, kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da wannan aiki a wasu kasashen Afirka 10 dake kunshe cikin shirin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China