in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya gana da mataimakin shugaban Sin Li Yuanchao
2017-05-12 10:29:36 cri
A jiya ne, shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao dake ziyara a Bujumbura, babban birnin kasar Burundi.

Li Yuanchao ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai da kasar Burundi a fannin siyasa, da cimma daidaito kan manufofin samun ci gaba, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin aikin gona, ayyukan more rayuwa da sauransu, da kara yin mu'amalar al'adu, da sa lura ga hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa, da sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu. Sin ta ce, ana samun kyautatuwar yanayin a kasar Burundi, tana kuma goyon bayan bangarori daban daban na kasar Burundi da su warware matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari.

A nasa bangare, shugaba Nkurunziza ya isar da gaisuwa zuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce, yanzu ana raya hadin gwiwar kasashen biyu yadda ya kamata, kuma ana aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kansu. Kana Nkurunziza ya jaddada nuna goyon baya ga manufar Sin daya tak a duniya, da matsayin Sin kan batun kudancin tekun kasar Sin da zirin Koriya. Kana ya taya murnar gudanar da taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19.

A yayin ziyarar, Li Yuanchao ya yi shawarwari tare da mataimakin shugaban kasar Burundi na farko Caston Sindimwo da na biyu Joseph Butore, inda suka duba yadda aka cimma yarjejeniyar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, kana ya yi bincike kan ayyukan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu tare da kai ziyara ga wasu iyalan dake wurin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China