in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da ministan harkokin wajen kasar Burundi
2017-03-16 14:53:59 cri

Yau Alhamis ne Li Yuanchao, mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da ministan harkokin wajen kasar Burundi Alain Aime Nyamitwe a nan Beijing.

A yayin ganawar, mista Li ya yi fatan cewa, kasashen Sin da Burundi za su kara inganta tsarin siyasa wajen raya huldar da ke tsakaninsu, tare da mai da hankali ga walwalar jama'a da kuma inganta mu'amala ta fuskar al'adu, a wani bangare na kokarin bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen 2.

A nasa bangaren kuma, Alain Aime Nyamitwe ya ce, kasarsa ta na fatan ganin ita da Sin za su mara wa juna baya, ta hanyar inganta hadin gwiwarsu ta fuskar aikin gona, ababen more rayuwa, makamashi, al'adu, kara taimakawa juna a al'amuran duniya da shiyya-shiyya, domin morar juna tare da samun nasara a tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China