Bankin duniya ya bayyana a ranar Litinin cewa, masana'antun kirkire kirkire da farfadowar al'adu a Afrika za su iyar taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki da rage talauci a nahiyar.
Darektar bankin duniya dake kasar Kenya, madam Diarietou Gaye, ta bayyana a yayin wani dandalin al'adu a birnin Nairobi cewa, arzikin wadannan bangarori yana yawan gasket, amma kuma har yanzu akwai yawancinsu ba'a fara amfani da su ba. Ya kamata Afrika ta kasance tare da duniya mai tafiyar da zamani ta hanyar nuna sabbin kirkire kirkire, ta yadda za ta iyar sayar da al'adunta ta hanyar amfani da fasahohin zamani, in ji madam Gaye a yayin taron kasa na masu ruwa da tsaki na bangaren ci gaban masana'antun bunkasa al'adu da kayayyakin gargajiya.
Taron na kwanaki biyu ya tattara mahalarta fiye da dari da suka zo domin sa kaimin raya al'adu da fasahohin kasar Kenya.
Madam Gaye ta kuma jaddada cewa, ya kamata Afrika ta yi koyi da sauran kasashe, domin samun gajiyar duniya ta bai daya. A cewarta, Afrika na da arzikin tarihin al'adu da gargajiya, fiye ma wata kila da sauran nahiyoyi. Kide-kide, dafuwa, kayayyaki jiki, harsuna, al'adu da addinan Afrika, dukkansu suna cikin wannan babban arzikin Afrika, in ji wannan jami'a ta bankin duniya. (Maman Ada)