in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta tabbatar da nadin sabon jagoran tawagar wanzar da zaman lafiya a CAR
2016-01-08 10:44:43 cri

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, ofishin babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya amince da nadin Parfait Onanga-Anyanga 'dan kasar Gabon, a matsayin jagoran tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a janhuriyar Afirka ta tsakiya CAR.

Dama dai Onanga-Anyanga, shi ke rike da wannan mukami a matsayi na wucin gadi tun daga ranar 16 ga watan Agustar bara, lokacin da Babacar Gaye daga Senegal ya mika takardar yin murabus daga shugabancin tawagar, biyowa bayan zargin da aka yiwa wasu daga jami'an rundunar na yiwa kananan yara fyade a janhuriyar Afirka ta tsakiyar.

Baya ga lalata da kananan yara, an kuma zargi wasu daga jami'an wanzar da zaman lafiyar da aikata wasu laifuka, wadanda suka sabawa dokokin aikin tawagar.

Kafin wannan mukami, Onanga-Anyanga ya wakilci MDD a tawagar lura da tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya, ya kuma kasance wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Burundi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China