in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci bangarorin kasar Libya dasu sa kishin kasa fiye da son zuciyarsu
2017-03-21 10:58:49 cri
Wakilin MDD a kasar Libya ya yi gargadi game da fargabar barkewar tashin hankali a fadin kasar ta arewacin Afrika sakamakon tura dakaru, lamarin da ke neman dagula al'amurran tsaro a babban birnin kasar Tripoli, da kuma fadan da ya barke kwanan nan a biranen Misrata da Benghazi.

Martin Kobler, wakili na musamman na sakatare janar na MDD a Libya, kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libya (UNSMIL), ya bukaci dukkan bangarorin Libya da ba sa ga maciji da juna da su hada kansu kuma su sa kishin kasarsu sama da son zuciyarsu.

A lokacin taron manema labarai, Martin Kobler, ya yi kira ga bangarorin Libya da kada su bari manufofin masu neman ta da rikici da tsattsauran ra'ayi ya wargaza kasar.

Jami'in ya buga misali da taron da aka gudanar na Quartet game da rikicin na Libya, wanda ya gudana a ranar 18 ga wannan wata, wanda ya nemi dukkan bangarorin kasar ta Libya dasu shiga shirin warware takaddamar siyasar kasar. Taron na Quartet ya hada da gamayyar kasashen larabawa, da kungiyar tarayyar Afrika AU, da tarayyar Turai da kuma MDD.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China