A jiya ne wani rukunin kamfanonin kasar Sin da ke hulda a Najeriya suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna ta kafa wani katafaren kafar talabijin na zamani wadda za ta rika watsa shirye-shiryenta a dukkan jihohin kasar.
Rukunin kamfanonin watsa shirye-shirye na Shandong Broadcasting Group Ltd, da Shandong Cable Interactive Service Ltd, da Inspur Group Ltd da kananan kanfanonin cikin gida da ke hulda da su, da rukunin kamfanin Innoson ne suka sanya hannun kan wannan yarjejeniya, bayan ganarwsu da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo a Abuja, fadar mulkin kasar.
A jawabinsa, Yemi Osinbajo ya ce yarjejeniyar ta zo a kan gaba, musamman irin gudummawar da za ta bayar ga bangaren tattalin arzikin kasar, baya ga samar da ayyukan yi ga matasan kasar.
Ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya za ta kafa wani kwamiti, wanda zai sa-ido kan yadda za a kara bunkasa hadin gwiwa, da kuma yadda za a aiwatar da tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.
Ana sa ran sanya kudaden da sassan biyu za su samar a cikin shekaru biyu masu zuwa a sassan tattalin arzikin kasar daban-daban.(Ibrahim)