in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutane 11 da ake zargi da satar mutane a Nijeriya
2017-04-26 09:36:15 cri

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta cafke wasu mutane 11 da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa a birnin Fatakwal na jihar Rivers, mai arzikin man fetur.

Kwamnadan sashen rundunar mai kula da ayyuka na musammam Abba Kyari, ya ce sun yi nasarar cafke mutanen da ake zargin ne sanadiyyar wasu bayannan sirri da suka samu.

Abba Kyari ya ce, sun gano cewa, wani tsohon ma'aikacin wani kamfanin man fetur dake aiki a Nijeriya da hadaddaiyar Daular Larabawa ne shugaban tawagar mutanen.

Ya ce, tuni mutumin ya tabbatar da cewa, yana daga cikin tsagerun yankin Neja-Delta dake kasar, kuma shi ya kitsa kisan da aka yi wa wani jagoran kungiyar tsageru a shekarar 2009.

Har ila yau, ya ce shi ne shugaban kungiyar da ta yi kaurin suna wajen sace likitoci da masana hada magunguna da wasu mazauna garin na Fatakwal tun daga shekarar 2015. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China