in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta jinkirta tattaunawar neman sulhu saboda rashin kudi
2017-04-10 09:47:47 cri

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce, an jinkirta tattaunawar neman sulhu a kasar, da aka shirya gudanarwa a watan Maris din da ta gabata, saboda rashin kudaden shirya taron.

Kakakin fadar shugaban kasar Ateny Wek Ateny, ya ce, an shirya gudanar da taron tattaunawar da shugaban kasar Salva Kiir ya sanar a watan Disamban bara ne da nufin bude wata kafa ta tattauna matsololin siyasa, zaman takewa da tattalin arziki da suka addabi kasar, tare da samar da hanyoyin warware su, da kuma sulhunta bangarori masu adawa da juna a kasar dake fama da rikici.

Ateny Wek, ya ce bayan jinkirin da aka samu na wata daya, taron zai gudana a wannan watan, saboda ma'aikatar kudi ta kasar, ta yi alkawarin fitar da kudaden da ake bukata.

Ya ce, an samu jinkirin ne saboda ma'aikatar ta kudi na kokarin samar da kudaden. Ya ce, samun kudi abu ne mai wahala, amma gwamnati na ba da tabbacin cewa, za a fara tattaunawar a wannan watan na Afrilu.

Sai dai, bangaren dake adawa da gwamnati na (SPLA IO) karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, ya soki lamarin taron, yana mai bayyana shi a matsayin wani shiri na siyasa domin jan hankalin dukkan bangarori su yi mubaya'a ga gwamnatin Kiir. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China