in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta baiwa baki ma'aikata a kasar wa'adi na biyan karin harajin aiki
2017-03-10 12:25:36 cri

Mahukunta a kasar Sudan ta Kudu, sun ja kunnen baki 'yan kasashen waje dake aiki a cikin kasar, da lallai su biya sabon kudin haradin aiki da aka ayyana, ko kuma su fice daga kasar.

Ministan watsa labarai na kasar Michael Makuei, ya shaida wa 'yan jaridu a birnin Juba, fadar mulkin kasar cewa, duk bakin da suka ki biyan kudin harajin da aka ayyana a makon jiya, za a tilasta masu barin kasar.

Bisa sabon tsarin kasar dai, baki masu manyan ayyuka da a baya ke biyan dalar Amurka 400, a yanzu za su biya dala 10,000. Wadanda ke yin matsakaitan ayyuka kuwa za su biya dala 2,000, yayin da masu aikin wucin gadi za su biya dala 1,000.

Mahukuntan kasar dai sun ce, sun dauki wannan mataki ne, domin dakile baki ma'aikata dake zaune cikin kasar masu goyon bayan wani tsagi na kasar, tun bayan barkewar rikicin shekarar 2013 wanda ya daidaita kasar. Kaza lika gwamnatin na fatan amfani da wannan manufa, wajen bunkasa harajin ta daga hanyoyin da ba na mai ba.

A watan Fabarairun da ya shude ne MDD ta bayyana kasar a matsayin wadda wasu sassan ta ke fama da matsanancin fari, sai dai kuma matakin da mahukuntanta suka dauka na kara harajin ma'aikata baki, na iya dagula ayyukan jin kai a irin wadannan yankuna.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China