Mahalarta taron suna ganin cewa, a shekaru 30 da suka wuce, ko da yake tattalin arzikin duniya na ta karuwa, kana yawan mutanen da suke fama da talauci na raguwa, amma duk da haka, akwai sauran rina a kaba, inda mutane fiye da miliyan dari 8 ke ci gaba da fama da matsanancin talauci. Don haka, ya zama dole wasu kasashen dake da koma bayan tattalin arziki su yi wa fannin aikin gona da tattalin arzikin kauyukansu kwaskwarima.
A nata bangare, kasar Sin ita ce ta zo ta farko daga cikin kasashe maso tasowa wajen cimma muradun karni na rage rabin yawan al'ummar kasar dake fama da talauci. Ganin haka, ya sa wani jami'in asusun raya aikin gona na IFAD ya ce, dabarar da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen rage talauci tana da amfani sosai, wadda dukkan al'ummun kasa da kasa suka tabbatar da hakan. A cewar jami'in, manufar da kasar Sin ta yi amfani da ita a fannin rage talauci, da nasarorin da kasar ta samu a wannan fanni, sun shaida cewa, muddin dai akwai kyakkyawar niyya da manufofin da suka dace, lalle akwai yiwuwar kawar da talauci gaba daya. Yadda kasar Sin ta samu nasara kan aikin kau da talauci ya zama abin koyi ga mutanen da suke yunkurin ciyar da aikin gaba a duk duniya.(Bello Wang)