in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Italiya yayi murabus
2016-12-05 11:00:07 cri
A jiya Lahadi, an jefa kuri'ar raba gardama a kasar Italiya dangane da batun gyaran kundin mulkin kasar. Sai dai kwarya-kwaryar sakamakon kidayar kuri'un da aka samar a yau Litinin da sassafe ya yi nuni da cewa, yawan kuri'un nuna rashin amincewa ya zarce na nuna yarda, wato ke nan an yi watsi da batun gyaran kundin tsarin mulkin kasar, don haka, firaministan kasar Matteo Renzi a yau Litinin ya sanar da yin murabus.

Gyaran kundin tsarin mulki da aka nema a wannan karo ya shafi gyaran tsarin siyasa da sassauta ikon majalisar dattawa da soke zaben 'yan majalisar da kuma shirin gwamnatin kasar na kwace iko daga hannun kananan hukumomi. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China