Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya, ta dage taron da ta shirya yi tsakanin kwamitin zartarwarta da 'yayan jam'iyyar dake majalisar dokokin kasar a ranakun 24 da 25 na wannan wata.
Kakakin jam'iyyar Bolaji Abdullahi, ya bayyana a jiya cewa, an dage taron ne saboda wasu abubuwa da suka taso, ya na mai cewa, za a sanar da sabuwar ranar idan lokaci ya yi.
A ranar 25 ga watan Junairun bana ne shugaban jam'iyyar APC John Odigie-Oyegun, ya kafa kwamiti mai kunshe da mambobi 10, domin sake nazarin kundin tsarin jam'iyyar.
Ana sa ran kwamitin zai yi nazarin kundin tsarin gabanin babban taron jam'iyyar da aka shirya yi cikin wannan wata.
Yayin taron karshe da kwamitin zartarwar jam'iyyar ya yi ne aka yanke shawarar yi wa kundin tsarin garambawul, da nufin magance matsalolin da suka shafi ladaftarwa da zama 'dan jam'iyya. (Fa'iza Mustapha)