in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yankewa wasu 'yan kungiyar Al-Shabaab su hudu hukuncin kisa
2017-04-25 09:42:56 cri

Wata kotun soji a Somalia ta yankewa wasu mayakan kungiyar 'yan tada kayar baya ta Al-Shabaab hukuncin kisa ta hanyar hari da bindiga, bayan da ta same su da laifin kaddamar da tagwayen hare hare, kan wani wurin cin abinci dake garin Baidoa, fadar mulkin jihar kudu maso yammacin kasar.

Da yake karin haske game da hukuncin, mataimakin jami'i mai shigar da kara Mumin Hussein Abdulahi, ya bayyanawa 'yan jarida cewa, an tabbatar mayakan ne suka kaddamar da harin ranar 28 ga watan Fabarairun bara, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80, tare da jikkata wasu karin mutanen 45.

Tuni dai aka harbe mutanen hudu wato Hassan Aden Mursal dan shekaru 23, da Abdiladhif Moalim Aden dan shekaru 34, da Siyad Hassan Farah dan shekaru 41, da kuma Sharmad Awow Mohamed mai shekaru 39.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China