in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia ta kaddamar da yaki a kan kungiyar Al-shabaab
2017-04-07 10:46:58 cri

Kwanaki biyu bayan harin tagwayen bam ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da raunata wasu 10, shugaban kasar Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed, ya kaddamar da yaki kan mayakan Al-Shabaab tare da yin tangade da rairaya a hukumomin tsaron kasar.

Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya nada tsohon jakadan kasar a Birtaniya Mohammed Ali Sanbaloolshe, a matsayin shugaban hukumar leken asiri, yayin da ya nada Jimale Irfid a matsayin sabon babban hafsan tsaro, a wani garambawul da ya dawo da Sanbaloolshen kan mukaminsa, shekaru uku bayan tsohon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud ya kore shi.

Shugaban kasar ya kuma dawo da tsohon shugaban rundunar 'yan sandan kasar, Abdihakim Dahir kan mukaminsa, inda ya kuma nada mataimakin jakadan kasar a Amurka, Thabit Mohammed Abdi matsayin magajin garin Mogadishu, kuma gwamnan yankin Banadir.

Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed ya shaidawa manema labarai a Mogadishu cewa, kasar ta kaddamar da yaki a kan mayakan Al-Shabaab, yana mai cewa, gwamanti ta ba su kwanaki 60 su mika wuya gare ta, inda za ta kyautata musu rayuwa.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China