in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 10 ne aka kashe a wani harin bam a Mogadishu
2017-04-10 09:06:40 cri

Mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da wasu sojoji, a sanadiyyar fashewar bam da aka adana cikin wata mota a kusa da ma'aikatar tsaron kasar Somaliya a Mogadishu, inda aka ba da rahoton harin da cewa, an so a kaddamar da shi ne kan wani babban jami'in soji.

Kamfanin dillancin labarai na SONNA ya ambato cewa, harin kunar bakin waken ya yi sanadiyyar lakume rayukan mutane 10 da kuma jikkata wasu da dama.

Tuni dai kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin harin na baya bayan nan a Mogadishu.

Kungiyar ta ce, ta yi nasarar hallaka sojojin gwamnati kimanin 10 a harin.

Wannan dai shi ne hari na biyu da kungiyar ta kaddamar cikin wannan mako a Mogadishu.

Wannan harin na zuwa ne bayan da shugaban kasar Somaliya ya umarci manyan hafsoshin sojin kasar da su kaddamar da shirin murkushe kungiyar Al-Shabaab daga doron kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China