in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ababan fashewa masu yawa sun hallaka mutane a Mogadishu
2017-04-17 09:52:27 cri

Mutane masu yawa sun rasa ransu a sanadiyyar fashewar bama bamai a kusa da filin jirgin sama na Aden Adde dake Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya a jiya Lahadi, shaidun gani da ido da jami'an tsaro sun tabbatar da afkuwar lamarin.

Wata mota makare da abubuwan fashewa mallakar mayakan kungiyar Al-Shabaab ne ta tada bama baman bayan jami'an tsaro sun damke ta a kusa da filin jirgin saman na Mogadishu.

Shaidun gani da ido da jami'an tsaro sun ce, lamarin ya faru ne bayan da aka yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaron kasar da mayakan a cikin birnin, lamarin da ya haddasa fashewar boma boman.

Wasu shaidun gani da ido sun ce, an harbi igogi masu luguden wuta 3 ne a kusa da filin jirgin saman da yankin Halane, sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM)

Wani mutum da ya ganewa idonsa faruwar lamarin wanda bai so a ambaci sunansa ba ya ce, a halin yanzu jami'an tsaron suna ci gaba da yin barin wuta kan mayakan 'yan tada kayar bayan, har ma sun yi nasarar kwace manyan bindigogi daga hannunsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China