in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco tana kokarin dawo cikin kungiyar tarayyar Afrika
2017-01-19 10:44:48 cri

Ministan harkokin wajen Morocco Salaheddine Mezouar ya bayyana cewa, dawowar kasar ta Morocco cikin kungiyar tarayyar Afrika (AU) batu ne dake da ma'ana ga nahiyar ta Afrika.

Mezouar ya shedawa 'yan jaridu bayan zaman da majalisar dokokin kasar ta yi, inda ta sake bibiyar kundin dokokin kungiyar tarayyar Afrika (AU), ya bayyana cewa, wannan mataki da kasar ta dauka zai ba ta dama wajen ba da gudumowarta ga ci gaban Afrika.

Ana sa ran a wannan makon ne majalisar dokokin kasar Morocco za ta zartar da doka kan wannan batu, gabanin fara taron koli na tarayyar Afrika wanda za'a gudanar tsakanin ranakun 22 zuwa 31 ga wannan wata, a helkwatar hukumar dake Addis Ababa, na kasar Habasha.

A ranar 10 ga wannan watan ne majalisar ministocin kasar ta tsara daftarin dokar, a wani mataki na kokarin sake mayar da kasar cikin kungiyar ta AU.

A shekarar 1984 ne Morocco ta fice daga kungiyar, kuma a watan Satumbar bara ne, ta gabatar da bukatar neman sake komawa kungiyar .

A 'yan makonnin nan, sarkin Morocco ya kai ziyarar aiki a kasashen Afrika da dama, domin neman goyon baya game da wannan aniya ta kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China