Ministan karafa da ma'adanai na Nijeriya Kayode Fayemi, ya ce a wani bangare na aiwatar da sauyi a banagaren hakar ma'adanai, nan da watannin shida, gwamnati za ta haramta fitar da ma'adanai da ba a sarrafa ba daga kasar.
Da yake jawabi yayin wani taro da ya gudana a Abuja, babban birnin kasar, Kayode Fayemi ya bayyana fitar da ma'adanai da ba a sarrafa ba daga kasar, a matsayin haramtaccen al'amari.
Ya ce, yadda mutane ke safarar ma'adanai daga kasar ne ya sanya gwamnati daukar matakin haramta fitar da wadanda ba a sarrafa ba.
Ya kuma yi bayanin cewa, gwamnati za ta karfafa wa masu hakar ma'adanai gwiwa, domin zuba jari a bangaren, ta hanyar kafa tashoshin sarrafa ma'adanan a yankunan dake da arzikinsu, domin samar da guraben aikin yi.
Kayode Fayemi ya ce, gwamnati ba za ta yi gaban kanta wajen aiwatar da haramcin ba, inda ya ce, za a ba masu sha'awar zuba jari isasshen lokaci na kafa tashoshin sarrafa ma'adanan. (Fa'iza Mustapha)