in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban COP22 ya jinjinawa Sin game da kokarinta na magance matsalar sauyin yanayi
2016-11-15 10:57:31 cri

Shugaban babban taro na 22 na masu ruwa da tsaki game da sauyin yanayi ko COP22, kuma ministan harkokin wajen kasar Morocco Salaheddine Mezouar, ya jinjinawa kwazon kasar Sin game da daukar matakai masu fa'ida, wadanda ke taimakawa wajen magance tasirin sauyin yanayi.

Mr. Mezouar wanda ke jawabi ga mahalarta wani kwarya kwaryar taro game da sauyin yanayi, yayin da ake ci gaba da shawarwari a babban taron sauyin yanayi na duniya dake gudana a kasar Morocco, ya ce, Sin na aiwatar da matakai na zahiri, baya ga rattaba hannu da ta yi kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Faris. Kaza lika jami'in ya ce, kasashe masu tasowa da dama na samun tallafi daga kasar, game da dabarun dakile tasirin sauyin yanayin.

Bugu da kari Mezouar, ya ce hadin gwiwar kasashen masu tasowa ya taimaka matuka, wajen cimma nasarar yunkurin da ake yi na shawo kan matsalar sauyin yanayi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China