in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa tsakanin Afrika da Sin da Amurka zai tabbatar da yakar fashin jiragen ruwa a Afrika
2016-07-28 10:11:25 cri

Babban jami'in MDD ya fada cewa, hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Amurka da kuma Afrika, zai iya yakar masu fashin jiragen ruwa a nahiyar Afrikar.

Wakili na musamman na MDD Mohamed Ibn Chambas, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin wani taron kwanaki biyu wanda aka kaddamar a jiya Laraba a birnin Lome na kasar Togo.

Ya ce, a ranar farko na taron hadin gwiwar tsakanin bangarorin uku, na Afrika da Sin da Amurka, sun gabatar da wasu hanyoyi da za su taimaka wajen tabbatar da kara hadin kai a tsakaninsu domin yakar fashin jiragen ruwa a Afrika.

Ya ce, kasar Sin da Amurka manyan kasashe ne biyu a duniya, kuma mambobi ne na kwamitin tsaro na MDD, kana dukkanninsu suna da kyakkyawar hulda da hadin gwiwa tsakaninsu da nahiyar Afrika, ya ce, idan har manyan kasashen biyu suka hada kansu, musamman wajen tabbatar da tsaro a harkokin teku, to hakika kasashen nahiyar Afrika za su amfana da kwarewarsu da fasaharsu wajen yakar fashin jiragen ruwa.

Chambas, wanda kuma shi ne shugaban hukumar lura da kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel, ya ce, akwai bukatar kasashen na Afrika su hada gwiwa da manyan kasashen domin magance kalubalen tsaro a tekunan da ake fuskanta a fadin nahiyar.

Ya kara da cewar, Sin da Amurka za su iya taimakawa Afrika wajen dakile safarar haramtattun kayayyaki da ake ta cikin tekuna na nahiyar ta Afrika, wadanda suka hada da tabar wiwi, da makamai, da man fetur, lamarin da ke matukar gurgunta ci gaba, da haddasa tashe tashen hankula a nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China