in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da Masar a fannonin ci gaba, in ji Yang Jiechi
2015-06-02 09:46:28 cri

Memba a majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, ya ce, kasarsa za ta ci gaba da tallafawa Masar, a yunkurinta na cimma daidaito, da samar da ci gaba a dukkanin fannoni.

Yang Jiechi wanda ke ziyarar aiki a Masar, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da shugaban kasar Abdel-Fattah al-Sisi, yana mai cewa, fannonin da kasashen biyu za su yi tarayya wajen neman bunkasuwa, su za dace ne da halin musamman da Masar din ke ciki.

Mr. Yang ya kuma alkawarta burin Sin na aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da sassan biyu suka daddale, tare da fatan daga matsayin dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.

Daga nan sai ya bayyana fatan hadin kan kasashen biyu, wajen bunkasa hadin gwiwarsu, karkashin manufar "ziri daya, hanya daya", wadda ta tanaji habaka samar da ababen more rayuwa, da kuma bunkasar masana'antu.

A nasa bangare, shugaba Sisi, bayyana godewar kasarsa ya yi bisa hadin kai da goyon baya da Sin ke nuna mata, yana mai jinjinawa irin ci gaban da Sin ta samu daga dukkanin fannoni. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China