in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen rukunin kasashe 7 da wakilan kasashe 5 dake yankin Gabas ta Tsakiya na tattaunawa kan batun Syria
2017-04-12 10:25:30 cri

Jiya Talata ministocin harkokin wajen rukunin kasashe 7 da wakilan kasashe 5 dake yankin Gabas ta Tsakiya wadanda suka hada da Turkiyya, hadaddiyar daular Larabawa, Saudiyya, Jordan, da Qwatar suna gudanar da wani taro a garin Luca dake kasar Italiya, inda suke tattaunawa kan batun game da yadda za a warware rikicin Syria ta hanyar siyasa.

A yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya bayan taron, ministan harkokin wajen kasar Italiya Angelino Alfano ya bayyana cewa, an samu babban sakamako yayin taron, kuma ya sake jaddada cewa, warware rikicin Syria ta hanyar siyasa dabara ce daya kacal da ta dace a yi amfani da ita.

Alfano ya ci gaba da cewa, yayin da ake kokarin warware rikicin Syria, ya kamata kasar Rasha ta kara sanya kokarinta, wakilai mahalarta taron su ma sun amince da ra'ayin.

Kana Alfano ya bayyana cewa, ya taba yin hira da ministan harkokin wajen Iran ta wayar tarho, inda ya nuna fatansa cewa, Iran za ta kara taka rawa a fannin, ta yadda za a hana sake kai hari kan fararen hula a Syria, tare kuma da hana yin amfani da makamai masu guba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China