in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Iran ya yi Allah wadai da matakin sojan da Amurka ta dauka kan Syria
2017-04-11 10:46:24 cri

Jiya Litinin shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya zargi kasar Amurka saboda ta harbi makamai masu linzami ga kasar Syria, inda ya bayyana cewa, matakin sojan da Amurka ta dauka ya nuna cewa, Amurka tana goyon bayan laifuffukan da 'yan ta'adda ke aikata a kasar ta Syria.

A yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya a wannan rana, shugaba Rouhani ya bayyana cewa, matakin sojan da Amurka ta dauka kan Syria ya sabawa dokar kasa da kasa, ya ci gaba da cewa, ba ma kawai matakin zai kawo illa ga shawarwarin neman sulhu a Syria ba ne, har ma zai samar da damammaki ga kungiyoyin ta'addanci domin su kara karfinsu.

Rouhani ya sake jaddada cewa, wajibi ne a warware rikicin Syria ta hanyar siyasa, kuma ya kamata al'ummar Syira su kansu su tsai da kuduri kan makomar kasarsu, bai kamata ba sauran kasashe su tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar. Rouhani ya ce, idan an gaskata cewa, 'yan ta'adda ne suka yi amfani da makamai masu guba yayin da suka kai hari a Syria, to, ta yaya Amurka za ta yi bayani kan batun ga kasashen duniya? (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China