in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta kusan rasa dukkan yankunan da ta mamaye a Iraki, in ji rundunar sojan kasar
2017-04-12 10:20:00 cri

Jiya Talata rundunar sojan kasar Iraki ta bayyana cewa, bayan kokarin da ake a ciki shekaru biyu da suka gabata, kawo yanzu, sojojin gwamnatin kasar sun riga sun kwace yawancin yankunan da mayakan kungiyar IS suka mamaye, ana iya cewa, kungiyar IS ta riga ta rasa kusan dukkan yankunan da ta mamaye a Iraki.

Kakakin ofishin ba da jagoranci kan aikin dakile ayyukan ta'addanci na kasar Iraki Yahya Rasool, ya gaya wa manema labarai cewa, ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2017, dukkan yankunan Iraki dake karkashin ikon IS sun riga sun ragu daga kaso 40 bisa dari a shekarar 2014 zuwa kaso 6.8 bisa dari a halin yanzu.

An ce, a halin yanzu, yankunan dake karkashin mamayar IS sun hada da unguwar yammacin birnin Mosul dake arewa maso yammacin kasar, da garin Tal Afar dake arewacin kasar, da garin al-Qaim dake yammacin kasar.

Kakaki Rasool ya bayyana cewa, an kwace unguwar dake gabashin Mosul daga hannun mayakan IS ne a watan Janairun bana, amma har yanzu unguwar dake yammacin birnin tana cikin hannun mayakan kungiyar IS bisa dalilin cunkuson jama'a.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China