Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar dakile wani harin da mayakan IS suka yi shirin kaiwa birnin Tikrit, inda suka kashe mayakan na IS guda 5.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, sojojin na Iraki sun yiwa mayakan IS luguden wuta da jirage masu saukar ungulu a yayin da suke kokarin shiga birnin, lamarin da ya tilasta musu janyewa zuwa yammacin hamadar Tikrit bayan dauki ba dadi na tsawon sa'o'i.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, 7 daga cikin sojojin sun jikkata, amma sun yi nasarar lalata motocin mayakan guda 4.
A daya hannun kuma an ci gaba da kazamin fada a kusa da Baiji, yayin da dakarun kasar ke kokarin fatattakar mayakan na IS daga matatar man Baiji wadda mayakan suka kwace wasu sassanta da dama.
Bangarorin biyu dai sun kwashe kusan wata guda suna arbatu a ciki da kuma kusa da garin na Baiji mai nisan kilomita 40 daga birnin Tikrit.
Tun ranar 10 ga watan Yunin shekarar da ta gabata, al'amuran tsaro suka yi matukar tabarbarewa a kasar ta Iraki, bayan barkewar wani mummunan fada tsakanin sojojin kasar da mayakan IS.(Ibrahim)