in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraqi sun kashe mayakan IS 200
2016-12-30 10:35:59 cri

A wani sabon harin da suka kaddamar, a kokarinsu na kwace iko da garin Mosul daga hannun mayakan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, a jiya Alhamis, dakatun Iraqi sun kwace wasu garuruwa da kauyuka dake makwaftaka da birnin Mosul, al'amarin da ya kai ga kisan mayakan IS kimanin dari biyu.

Wata sanarwa daga rundunar hadin gwiwa ta Iraqi ta ce, dakarun sashen yaki da ta'addanci, sun kai hari kan mayakan IS a wani gari dake makwaftaka da gabashin Mosul, inda suka kwace garin Al-Quds, sannan aka ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun da mayakan IS a sauran garuruwa makwafta.

Sanarwar ta kara da cewa, dakarun runduna ta 16, sun kwace iko da kauyukan Al-Sada da Tawiyla, inda suka kafa tutocin kasar Iraqi a muhimman gine-gine.

Har ila yau, a kudu maso gabashin birnin Mosul, 'yan sanda da hadin gwiwar sojojin runduna ta 9, sun kai hari kan mayakan IS a yankuna uku da suka hada da Al-Entisar da Al-Salam da kuma Al-Shaimaa, inda aka yi ta bata kashi tsakanin su da mayakan na IS. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China