in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 31 sun mutu a gumurzu da IS a yankin Anbar na Iraki
2015-09-28 10:45:48 cri

An kashe a kalla mutane 31 a ranar Lahadi a cikin gumurzu tare da mayakan kungiyar IS a yankin Anbar, dake yammacin kasar Iraki. Harin mafi muni ya faru ne a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka kutsa da motocinsu dauke da boma bomai a sansanin soja dake kunshe da sojojin Iraki da mayakan sa kai dake mara musu baya da ake kira Hachd Chaabi, a gabashin birnin Falloujah mai tazarar kilomita 50 daga yammacin Bagadaza dake hannun kungiyar IS, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da kuma mayakan sa kai 12, a cewar wata majiyar tsaro a wurin, da ta bukaci a sakaya sunanta.

Fashewar boma-bomai sau biyu sun biyo bayan gumurzu tare da mayakan kungiyar IS kusan goma, in ji wannan majiya, inda ta kara da cewa, ba a tantance adadin mayakan kungiyar IS da suka mutu ba, amma an kashe da dama daga cikinsu, da jikkata wasu a cikin gurmurzun. (Maman Ada) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China