in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tattaunawa game da shirin tsakaita bude wuta na Syria a Astana
2017-02-07 09:20:37 cri

Kasashen Rasha, Turkiyya, Iran da Jordan sun yi tattaunawa game da sa ido kan cikakken aiwatar da shirin tsakaita bude wuta na Syria a jiya Litinin, wanda kuma ya samu halartar jami'an MDD.

Mahalarta taron sun amince da daukar ingantattun matakai na sa ido, don tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar tsakaita bude wutar game da rikicin na Syria, shugaban tawagar wakilan kasar Rasha dake halartar taron, kuma mataimakin babban jami'in gudanar da tsare tsare na kasar, Major Janar Stanislav Gadzhimagomedov, ya tabbatar da hakan bayan kammala taron a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan.

Mahalarta taron sun tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa domin ganin an cimma nasarar aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar tsakaita bude wutar tsakanin bangarorin dake yaki da juna a Syria.

Sai dai kuma, kamar yadda mahalarta taron suka nuna, batun shirin tsakaita bude wutar na Syria, yana fuskatar katsa landan daga kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China