in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin ruwan Sin ta ceto jirgin ruwan Tuvalu daga 'yan fashin teku a mashingin ruwan Aden
2017-04-10 11:10:05 cri

Tawagar jiragen ruwa da rundunar sojin ruwa ta dakarun sojin kasar Sin (PLA) ta tura, ta ceto jirgin ruwan Tuvalu daga hannun 'yan fashin teku a mashigin ruwa na Aden a jiya Lahadi.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ruwan ta fitar, ta ce tawagar jiragen ruwanta na 25, dake aikin ba da kariya a mashigin ruwa na Aden da kuma tekun Somaliya, ta samu rahoton sace wani jirgin ruwa mai lamba OS35 da misalin karfe 5 na yammacin Asabar, inda nan take jirgin ruwa na Yulin ya kama hanyar zuwa don kai dauki.

Bayan nazari da samun bayanai tare da tuntubar matuka jirgin ne aka fara aikin ceto da sanyin safiyar jiya Lahadi.

Ayarin sojojin ruwa 16 na runduna ta musammam ne suka bi jirgin OS35 tare da ceto matukan jirgin 19.

Sanawar ta ce, dukkan matukan 19 na karkashin kulawar rundunar sojin ruwan Sin, kuma sojojin sun gudanar da binciken tsanaki cikin jirgin, domin tabbatar da babu sauran barazanar tsaro. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China