in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya za ta kafa dokar yaki da 'yan fashin teku
2017-02-07 08:51:58 cri

Mahukuntan Najeriya sun lashi takobin kafa wata doka ta musamman, wadda za ta yaki daukacin ayyukan masu fashin teku, da masu aikata sauran laifuka a ruwayen kasar.

A cewar shugaban hukumar dake lura da al'amuran da suka shafi tekun kasar NIMASA Mr. Dakuku Peterside, sabuwar dokar da a yanzu ke gaban ma'aikatar shari'ar kasar domin nazartar ta, ta tanaji matakan tsaftace sashen sufurin ruwan Najeriya, ta yadda sashen zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.

Mr. Peterside wanda ya bayyana hakan a birnin Fatakwal dake jihar Rivers a kudu maso gabashin Najeriya ya kara da cewa, ta hanyar tabbatar da dokar, Najeriya za ta samu zarafin matsa kaimi wajen sanya ido, da tattara bayanan sirri a ruwayen kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China