in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki jirgin ruwan dakon mai da 'yan fashin tekun Somaliya suka sace
2017-03-17 10:49:20 cri

A daren jiya Alhamis, kungiyar yaki da 'yan fashin teku ta sanar a shafinta na yanar gizo cewa, an riga an saki jirgin ruwan dakon mai samfurin "Aris 13", kuma ma'aikatan dake cikin jirgin suna cikin koshin lafiya.

Jagoran shirin yaki da 'yan fashin teku na yankin arewa maso gabashin Afirka John Steed shi ma ya sanar da labarin a shafin yanar gizo, inda ya bayyana cewa, jirgin ruwan yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Bosaso dake bakin tekun kasar Somaliya.

Kafofin watsa labarai na kasar ta Somaliya sun ba da labari cewa, manyan dattijai a Puntland da jami'an gwamnatin wurin sun yi tattaunawa da 'yan fashin tekun, daga baya 'yan fashin tekun sun amince da sakin jirgin.

A ranar 13 ga wata ne, aka sace wani jirgin ruwa mai dakon mai samfurin "Aris 13" na wani kamfanin Daular Larabawa a kan teku dake arewa maso gabashin kasar Somaliya, a lokacin da jirgin ruwan yake kan hanyarsa daga kasar Djibouti zuwa birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar ta Somaliya, gaba daya akwai ma'aikata 8 'yan asalin kasar Sri Lanka suna cikin jirgin.

A jiya kuma dakarun kiyaye tsaron kan teku na karamar gwamnatin garin Puntland na kasar Somaliya sun yi musanyar wuta da 'yan fashin teku wadanda suka sace jirgin ruwan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China