in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun gwamnatin Somaliya sun yi musayar wuta da 'yan fashin teku
2017-03-17 10:43:16 cri

Jiya Alhamis dakarun kiyaye tsaron kan teku na karamar gwamnatin garin Puntland na kasar Somaliya, sun yi musanyar wuta da 'yan fashin teku wadanda suka shiga aikin sace jirgin ruwa mai dakon mai.

Wani jami'in unguwar Alula ta jihar Bari dake arewa maso gabashin garin Puntland Ali Shire Mohamud, ya fadawa manema labarai cewa, a wannan rana, wani jirgin ruwan 'yan fashin teku yana samar da kayayyaki ga wani jirgin ruwan dakon mai da 'yan fashin teku suka sace, a daidai wannan lokaci, dakarun kiyaye tsaron kan teku na Puntland sun tarar da su, har sun yi musanyar wuta tsakaninsu.

A daren jiya, jagoran shirin yaki da 'yan fashin teku na yankin arewa maso gabashin Afirka John Steed ya gayawa wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho a birnin Neirobi na kasar Kenya cewa, da gaske ne an yi musanyar wuta a kan tekun, amma kawo yanzu ba a san yawan mutanen da suka rasa rayuka ko suka ji rauni ba.

A ranar 13 ga wata, aka sace wani jirgin ruwa mai dakon mai na wani kamfanin Daular Larabawa a kan teku dake arewa maso gabashin kasar Somaliya, a lokacin, jirgin ruwan yana kan hanyarsa daga kasar Djibouti zuwa birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar ta Somaliya, gaba daya akwai ma'aikata 8 'yan asalin kasar Sri Lanka dake cikin jirgin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China