in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurkawa na mai da hankali kan ganawar Xi da Trump
2017-04-07 10:50:56 cri

Yanzu Amurkawa na mai da hankali matuka kan ganawar da shugabannin biyu za su yi, kuma suna fatan shugabannin biyu za su yi musayar ra'ayoyi kan batutuwa a jere dake shafar sassan biyu da shiyya shiyya da kuma kasashen fadin duniya.

Kakakin fadar "White House" Sean Spicer ya taba bayyanawa a yayin taron ganawa da manema labarai a karshen watan Maris da cewa, shugabannin kasashen biyu za su yi musayar ra'ayi kan muhimman ayyukansu, kuma za su samar da wani jadawalin raya huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Shehun malamin jami'ar Harvard ta Amurka Joseph S. Nye ya bayyana cewa, cudanya tsakanin shugabannin Sin da Amurka tana da muhimmanci matuka, yana fatan ganawar da za su yi za ta nuna wa al'ummomin kasashen duniya cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka yana da babbar ma'ana, har zai kawo alheri ga sassan biyu.

Shugaban jihar Colorado ta Amurka John Hickenlooper ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya, yana fatan shugaba Trump zai mayar da kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar yin hadin gwiwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China