in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara tattaunawa tsakanin wakilan Sin da Amurka game da harkokin cinikayya
2014-12-19 10:00:50 cri

Wakilan kasashen Sin da na Amurka na tattaunawa a birnin Chicagon kasar Amurka, a wani mataki na bunkasa hadin gwiwar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, karkashin dandalin habbaka cinikayya da kasuwanci na JCCT.

Cikin mahalarta dandalin tattaunawar na bana, akwai mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, da magatakardar sashen harkokin cinikayyar kasar Amurka Penny Pritzker, da kuma wakilin kasar a fannin ciniki Michael Froman.

A jawabinsa na maraba, Mr. Wang Yang, ya zayyana kadan daga muhimmancin taron wanda shi ne irin sa na 25 da bangarorin biyu ke gudanarwa, yana mai cewa, taron wani ginshiki ne na lalubo hanyoyin bunkasa harkokin tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka cikin shekara mai kamawa, da ma nan gaba.

Mr. Wang ya kuma yi kira ga sassan biyu da su hada gwiwa da juna, wajen kau da duk wani shinge, da ka iya zama cikas ga hadin kan dake tsakanin su, tare da binciko karin hanyoyin bunkasa hadin gwiwa.

Shi kuwa a nasa jawabi, sakataren harkokin cinikayyar Amurka Penny Pritzker karfafa kalaman Mr. Wang ya yi, yana mai cewa, kasashen biyu su ne mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kuma sauyin da kasar Sin ta samu zai taimaka matuka, wajen samar da damammakin kasuwanci a fannoni daban daban, a kuma dukkanin fadin duniya.

An dai kafa wannan dandali na JCCT ne a shekarar 1983, wanda kuma kawo yanzu ke zamansa sau daya a ko wace shekara. An kuma gudanar da taron dandalin na bara ne a nan birnin Beijing. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China