Jiya Alhamis ministan baitulmalin kasar Amurka Jacob Lew ya halarci taron kara wa juna sanin da cibiyar yin nazari kan kamfanonin Amurka ta shirya a birnin Washington, inda ya bayyana cewa, tun daga yanzu har zuwa watan Satumban bana, an shiga lokaci mai muhimmanci na gudanar da shawarwari kan BIT, yarjejeniyar zuba jari tsakanin sassan biyu wato Sin da Amurka.
Wannan rana, Jacob ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu za su yi ganawa da juna a birnin Beijing na kasar Sin a watan Satumban bana, lamarin zai jawo hankulan jama'ar kasa da kasa, shi ya sa, daga yanzu zuwa watan Satumba, ya kamata tawagogin yin shawarwarin na sassan biyu su yi amfani da wannan dama domin samun ci gaba.
Jacob ya kara da cewa, yarjejeniyar BIT da za a daddale za ta amfanawa kasashen biyu, kana ya bayyana cewa, a cikin wannan mako, tawagogin sassan biyu za su kara gudanar da wasu shawarwari tsakaninsu a Washington. Amurka tana sa ran Sin za ta cimma burin kyautata tsarin tattalin arzikinta, saboda Amurka za ta samu moriya daga wajenta, kuma Amurka tana fatan Sin za ta kara samun wadata da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba da taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasa da kasa.(Jamila)