Gwamnatin jihar Yobe dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana aniyarta ta tantance adadin yankunan da rikicin Boko Haram ya illata domin sake ginawa da kuma farfado da su.
Musa Jidawa, shi ne jami'in kwamitin dake kula da shirin farfado da yankunan, ya fada a Damaturun jihar Yoben cewa, shirin ya kunshi da samar da abinci, har ma da wanda ba na abinci ba, ya hada da samar da ruwan sha mai tsabta, da samar da wuraren kwana, da kiwon lafiya, ilmi, da kuma kare mutanen dake rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira.
Jidawa ya ce, an gabatar da shirin ne a lokacin wani taron karawa juna sani wanda gwamnatin jihar ta shiryawa masu ruwa da tsaki game da ayyukan samar da jin kai a jihar.
Shirin farfadowar, ya hada da raya aikin gona da samar da kayan aiki da ba da horo ga sana'o'i.
Ya ce, taron karawa juna sanin ya tabo batun dalilan dake haddasa yawan rikice rikice da kuma nazartar hanyoyin dakile su, a matsayin wani bangare na tada komada da kuma kafa cibiyoyin sauya tunanin mutanen da tashe tashen hankula ya shafa, musamman game da duba tunaninsu, da lafiyarsu da kuma warware matsalolin dake addabar mazauna sansanonin 'yan gudun huijirar.(Ahmad Fagam)