Hukumonin Najeriya sun ba da sanarwa a jiya Laraba cewa, za a gudanar da bincike kan wasu mutane 10 da aka kama su da laifin rarrabawa 'yan gudun hijira haramtattun kwayoyi.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA, ta ce ta kama wasu 'yan gudun hijira 60 wadanda take zargi da laifukan ta'ammali da haramtattun kwayoyin a wasu sansanonin 'yan gudun hijira 5 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ona Ogilegwu, shugaban hukumar yaki da haramtattun kwayoyi a jihar Borno, ya shedawa 'yan jaridu cewa, mutane 84 tuni ana tsare da su wadanda ake zargin su da hannu wajen ta'ammali da haramtattun kwayoyi.
Wasu daga cikin mutanen, an damke su ne tun a watan Janairu da kuma farkon watan nan na Maris.(Ahmad Fagam)