in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ANC za ta gana da jami'yyun kawance game da kiran da ake wa shugaba Zuma ya sauka daga mulkin kasar
2017-04-06 10:45:07 cri

Jam'iyya mai mulkin Afrika ta Kudu ANC, ta ce za ta gana da jama'iyyun kawance, domin tattaunawa kan kiran da ake yi wa shugaban kasar Jacob Zuma ya yi murabus.

Sakataren janar na jam'iyyar ANC Gwede Mantashe ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a jiya Laraba, game da taron kwamitin gudanarwar jami'iyyar NWC da aka yi ranar Talata.

Ko a ranar Litinin manyan jami'an jam'iyyar ANC sun gudanar da wani taro, domin nazari kan sauyin da shugaban ya yi a majalisar zartarwarsa a makon da ya gabata.

ANC dai na kawance ne da jami'yyar kwaminisanci na kasar SACP da kungiyoyin kwadago na COSATU.

Mantashe ya ce, kwamitin NWC ya jadadda bukatar ANC ta hada hannu da kawancenta domin amfanin kasar, inda ANC ta bi sahun kiraye-kirayen da SACP da COSATU da sauran jam'iyyu ke yi, dake neman shugaba Jacob Zuma ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban jamhuriyar Afrika ta Kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China