in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta bayyana Akbarzhon Dzhalilov a matsayin maharin birnin St. Petersburg
2017-04-05 08:59:39 cri

Hukumar bincike ta Rasha RIC, ta bayyana Akbarzhon Dzhalilov mai shekaru 22 a matsayin wanda ya kai wa jirgin kasa hari a birnin St. Peterburg da tsakar ranar Litinin.

Harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 14 tare da raunata wasu da dama, ya auku ne a cikin jirgin karkashin kasa, a lokacin da yake kan hanya tsakanin tashoshinsa biyu na birnin St. Petersburg, da shi ne birni mafi girma na biyu a kasar.

Sanarwar da hukumar RIC ta fitar, ba ta bayyana ko Dzhalilov yana da abokan hulda, ko kuma yana da alaka da kungiyar IS ko wata kungiyar ta'addanci ba.

Kamfanin dillancin labarai na Interfax ya ruwaito kakakin hukumar RIC Svetlana Petrenko na cewa, Dzhalilov da kansa ya mutu a harin.

A shekarar 2011 ne Akbarzhov Dzhalilov tare da iyayensa suka koma Rasha da zama daga Kyrgyzstan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China