in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta la'anci harin bom da aka kai a Rasha
2017-04-04 17:21:51 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana cewa, Sin ta nuna matukar takaici gami da yin tofin Allah tsine kan harin bom da aka kai a layin dogo na karkashin kasa a birnin St. Petersburg dake kasar Rasha. Madam Hua ta ce, kasar Sin ta nuna babban alhini ga wadanda suka rasa rayukansu, da jajantawa iyalan mamatan.

Ta ce kowane dan Adam na adawa da ta'addanci. Kuma kasar Sin na son karfafa hadin-gwiwa tare da Rasha, da shawo kan barazana gami da kalubalen harin ta'addanci, a kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya baki daya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China