in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na matukar Allah wadai da harin birnin London
2017-03-23 19:15:40 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar ta na matukar Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar a kusa da ginin majalissar dokokin Birtaniya dake birnin London.

Hua ta ce kasar Sin na mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar harin, da kuma jaje ga wadanda suka jikkata. Ta ce Sin na adawa da duk wani nau'in aikin ta'addanci, kasancewa su hanya ta nuna kiyayya ga daukacin kasashen duniya.

Kaza lika jami'ar ta kara da cewa, Sin za ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa ciki hadda Birtaniya, wajen yaki da ayyukan ta'addanci, tare da bada gudummawa ta wanzar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da sauran batutuwa na tsaron duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China