in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ANC ta yi Allah-wadai da ziyarar da magajin garin Tshwane ya kai yankin Taiwan
2017-01-03 09:46:21 cri

Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afirka ta kudu ta bayyana rashin jin dadinta dangane da ziyarar baya-bayan da magajin garin Tshwane(Pretoria) Solly Msimanga ya kai yankin Taiwan na kasar Sin, tana mai cewa, hakan tamkar rashin martaba kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta kudun ne.

Wata sanarwa da jam'iyyar ANC ta fitar ta bayyana cewa, magajin garin Tshwane, shi ne babban jami'in gwamnatin Afirka ta kudu da ya amince da matsayin Taiwan a matsayin kasa, duk da cewa, birnin Tshwane ba jiha ce mai cin gashin kanta ba, don haka ANC ta ce ta dauki wannan mataki ne bisa radin kanta.

A lokacin hutun kirsimati ne dai Msimanga 'dan jam'iyyar adawa ta DA ya ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, matakin da ya saba manufar Sin daya tak a duniya da gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta amince da ita.

ANC dai ta bayyana damuwa cewa, jam'iyyar adawa ta DA tana yunkurin tafiyar da wata gwamnati ce ta hanyar amfani da manufofinta na kasashen waje, ba tare da la'akari da manufar gwamnati, da martabar kasar a idon duniya, da kuma harkokin tsaron kasar ba.

Wannan ziyara ta Msimanga dai ta fuskaci soka daga bangarori da dama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China