in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda: jimillar GDP ta kai 5.9% a shekarar 2016
2017-03-20 13:15:56 cri

Kafofin yada labaru na kasar Rwanda sun labarta a kwanan baya cewa, karuwar jimillar kudaden da aka samu daga sarrafa dukiyoyin kasar Rwanda wato GDP, ya kai kashi 5.9 cikin dari a shekarar 2016, adadin da ya yi kasa da wanda ma'aikatar kudin kasar, da ma asusun ba da lamuni na duniya wato IMF suka yi hasashe, wato kashi 6 cikin dari. Haka kuma adadin yi kasa da karuwar GDPn kasar na shekarar 2015, wato kashi 6.9 cikin dari.

Kafofin yada labarun kasar sun yi bayanin cewa, muhimmin dalilin da ya sa aka samu raguwar jimillar GDPn a bara shi ne, rashin girbin hatsi wadatacce sakamakon bala'in fari da ambaliyar ruwa da aka yi fama da su a karshen rabin shekarar ta bara.

Har ila yau kuma, a bara, karuwar bunkasuwar masana'antu da aikin ba da hidima ya kai kashi 7 cikin dari bisa na shekarar 2015, lamarin da ya kara bunkasa tattalin arzikin kasar ta Rwanda a shekarar 2016 da ta gabata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China