in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta:Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Rwanda
2017-03-18 13:35:44 cri

A juma'ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabannin biyu suka amince da inganta tsarin hadin gwiwa, da kuma daukaka hadin gwiwar a tsakanin kasashen biyu, a yayin da ake tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, wanda aka gudanar a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu.

Mr.Xi Jinping ya jaddada cewa, ainihin manufar da ya gabatar a yayin da ya kai ziyara kasashen Afirka a shekarar 2013 shi ne, hada cigaban kasar Sin da cigaban Afirka, domin tabbatar da hadin gwiwar samun moriyar juna da kuma ci gaban juna. Kasar Sin ba ma kawai ta kasance wadda ke sa kaimin samun dauwamammen ci gaban Afirka ba ne, har ma ta kasance jagora a fannin aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka a duniya baki daya. Duk da sauye-sauyen dake faruwa a duniya, kasar Sin ba za ta canza manufarta kan kasashen Afirka ba. Baya ga haka, kasar Sin za ta hada kan kasashen Afirka wajen tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

Mr.Kagame a nasa bangare ya bayyana cewa, Rwanda na yabawa kasar Sin kan manufarta ta sada zumunta da kasashen Afirka, da kuma yadda take tsayawa ga zaman daidai wa daida, da girmama juna, a yayin da take bunkasa huldarta da kasashen Afirka, da kuma yadda ta ke kokarin bunkasa hadin gwiwa a tsakaninta da Rwanda da ma sauran kasashen Afirka bisa ga sakamakon da aka cimma a gun taron kolin Johannesburg.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China