in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na sahun gaba a Afirka a fannin janyo masu sha'awar zuba jari
2017-01-17 10:46:41 cri
Wani rahoton bincike game da karfin kasa ta fannin gogayya a duniya na shekarar 2017 (GTCI), ya nuna cewa, kasar Rwanda tana daga goma na farko cikin kasashen da ke yankin kudu da hamadar Sahara a wannan fanni.

Rahotan wanda aka wallafa jiya a birnin Davos na kasar Switzerland, ya yi amfani da alkaluman yadda kasa ta bunkasa, da yadda ta ke janyo da kuma rike kwararrunta, yadda ta ke taimakawa masananta da matakan da za su bunkasa kwarewarsu ta yin takara.

GTCI dai ta gudanar da bincikenta ne a kan kasashe 118, inda ta yi bitar tasirin canje-canjen fasahar zamani a fannin kwarewar gogayya. Kuma kasar Rwanda ce ta 6 inda kwararru suka fi yin takara a kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara, kana kasa ta 91 a duniya a wannan fannin inda ta samu kaso 36.76 cikin 100

Kasar Mauritius ce ta ke kan gaba a kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara, sai kasashen Botswana da Afirka ta kudu da ke biye da ita.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China