Kasar Sin za ta kafa wata gidauniya ta musammun ta kudin RMB biliyan 60 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9,4 domin tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu (SME), in ji gwamnatin kasar a ranar Talata.
Wannan gidauniya tana da manufar rage matsalolin kudi na wadannan masana'antu, karfafa kokarinsu domin bunkasa huldar kasuwanci da kirkire kirkire, tare kuma da kafa wani sabon yunkurin bunkasuwa, a cewar wata sanarwar da aka fitar bayan wani babban taron kwamitin kula da harkokin kasa da faraminista Li Keqiqng ya jagoranta. (Maman Ada)