A ranar 8 ga watan da muke ciki ne bankuna a Nijeriya suka kusa kwace harkokin kamfanin sadarwa na Etisalat, ba dan babban bankin kasar CBN da hukumar kula da kamfanonin sadarwa sun sa baki ba.
Kamfanin sadarwa na Etisalat mallakar hadaddiyar daular Larabawa, wanda ya fara aiki a Nijeriya a shekarar 2009, ya kusa rasa ikonsa ne biyo bayan dimbin basussuka da bankuna ke binsa.
Bashin da bankunan ke bin kamfanin ya kai dala biliyan 1.72.
kamfanin Etisalat shi ne kamfanin sadarwa mafi girma na hudu a Nijeriya, inda adadin masu amfani da layin kamfanin ya kai miliyan 21 a cikin watan Junairun bana.( Fa'iza Mustapha)